Hukumar EFCC na zargin ana mata yankan baya

Shugabar EFCC, Farida Waziri
Image caption Shugabar EFCC, Farida Waziri

Hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin Najeriya ta'annati, EFCC, ta koka kan yunkurin da ta ce wasu fitattun 'yan kasar suna yi, wajen ganin sun jefa ayyukanta cikin rudani, yayin da babban zaben kasar ke karatowa.

EFCC ta zargi mutanen, wadanda ba ta bayyana sunansu ba, da fitar da bayanan karya a kan shugabar hukumar, Mrs Farida Waziri, da kuma ayyukanta.

A cewar hukumar EFCC, wata hanya ce ta sanyaya mata gwiwa, a yakin da ta ke yi da matsalar cin hanci da rashawa a Najeriyar.

A cikin wata hira da BBC, kakakin EFCC Mr Femi Babafemi, ya ce kamata yayi jama'a su kawo goyon bayansu ga hukumar, saboda irin nasarorin da ta samu tun bayan kafa ta.