Kananan hukumomin Najeriya na kokawa

Taswirar Najeriya
Image caption Taswirar Najeriya

A Najeriya, ana ci gaba da kace-nace game da asusun hadin gwiwa na jihohi da kananan hukumomi.

Shugabannin kananan hukumomin dai na zargin gwamnatocin jihohinsu da zaluntarsu a wannan asusu ta hanyar zaftare kudaden nasu, zargin da gwamnatocin jihohin suke musantawa.

Ba kasafai shugabannin kananan hukumomi kan yi magana a kan halin wannan asusu ba; amma Shugaban Karamar Hukumar Kanam da ke Jihar Filato a arewacin kasar, Dokta Sale Muhammad, ya shaidawa wakilin BBC cewa shi bai ma san nawa gwamnatin tarayya ke baiwa karamar hukumarsa ba.

“In da za ka yi bincike a duk Najeriya, watakila ba shugaban karamar hukumar da zai iya gaya maka cewa ga takardar bayanin asusun da ya taba samu [ko da] sau daya”, inji Dokta Sale.

Shugaban na Karamar Hukumar Kanam ya kuma kara da cewa kafin a kira su taron hadin gwiwa a kan kudin da ke cikin asusun kamar yadda doka ta tanada, “za ka samu an riga an kashe rabin wadannan kudaden—wai akwai kudaden da ya kamata [kananan hukumomin su] biya saboda gudanar da wasu abubuwa, an riga an cire a madadinku kafin a yi zama a kan abin da ya saura.

“Shi din ma kuma kafin ya zo hannun [kananan hukumomin sai] an sake cire wadansu abubuwa”.

Sai dai gwamnatin Jihar Filato ta musanta zargin zaftare kudaden ta bakin Kwamishinan Harkokin Kananan Hukumomi da Masarautu, Mista Chris Hasan.

A cewarsa, “tun zuwan gwamnati mai ci, ba a taba daukar ko sisi ba na kananan hukumomi.

“A yadda ake kashe kudin gwamnati ana tabbatar da toshe duk wata kofa ta almundahana”

Shi dai wannan asusu, gwamnatocin jihohi ne kan bude shi a bankuna, inda a kan zuba kason kudaden wata-wata na kananan hukumomin daga baitulmalin gwamnatin tarayya, kafin daga bisani kuma a baiwa kananan hukumomin.