Al-Shabaab ta hade da Hizbul Islam

Image caption Mayakan kungiyar, Al-shabab

A karshen makon da ya wuce ne aka bada sanarwar cewa daya daga cikin manyan kungiyoyi masu gwagwarmaya da makamai a Somaliya, Hizbul Islam zata narke ta shiga cikin kungiyar 'yan gwagwarmaya ta al-Shabaab da ta fita girma.

A da dukkan kungiyoyin biyu na ta fafutukar ganin sun tumbuke gwamnatin Somaliya ce wadda dakarun kungiyar tarayyar Afrika ke baiwa kariya.

Abin tambaya a nan shi ne ko wane muhimmanci wannan hada karfi tsakaninn 'yan adawar yake da shi

Kungiyar masu fafutuka ta Hizbul Islam ta dade tana fuskantar matsin lamba ta fuskar soji daga Al Shabab. A yanzu taba da kai bori ya hau. Masu lurra da al'amura na ganin wannan mataki ba wani abu bane illa dai kasawa ta fuskar soji.

Ba lallai bane wannan mataki ya kawo sauyi a halin da ake ciki a birnin Mogadishu, inda sojojin kiyaye zaman lafiya na Tarayyar Afrika ke bada kariya ga gwamnatin rikon kwarya ta kasar.

Sojojin kiyaye zaman lafiyar dai ba su da karfin kama baki dayan birnin na Mogadishu, amma suna da karfin hana kungiyoyin masu tada kayar bayan cimma burinsu na kawar da gwamnatin baki daya.

Mai magana da yawun sojojin kiyaye zaman lafiyar Major Bahoku Barigye, ya gayawa BBC cewa hadewar kungiyoyin na Alshabab da Hizbul Islam, ba zai haifar da komai ba. Yana mai cewa dakarunsa sun sha fuskantar hari daga kungiyoyin biyu a lokuta guda.

Ana yiwa Al Shabab wacce keda mayaka 'yan kasar waje, kallon kungiya mafi tsauri a kan Hizbul Islam. Duka dai suna fama da matsalar rikicin shugabanci, abinda yasa wasu ke ganin ba abin mamaki bane idan kawancen ya watse nan da 'yan kwanaki kadan.