Kamfanin Chevron ya dakatar da fitar da mai a Najeriya

Kamfanin mai na Chevron ya bayyana cewa ya dakatar da fitar da mai a wani bututunsa dake yankin Naija Delta a Najeriya sakamakon wani hari da aka kai masa a karshen mako.

Kamfanin ya ce an kai wa bututun da ke yankin Dibi-Abiteye na jihar Delta hari ne a ranar Juma'ar da ta gabata..

A wata sanarwa da ya aike wa kafofin yada labarai a yau, kamfanin Chevron ya ce ya dakatar da fitar da mai ta bututun da aka kai wa hari ne domin bincika irin barnar da aka yi wa bututun.

Sai dai kamfanin bai bayyana yawan man da za a dakatar da fitarwa ba sakamakon al'amarin da ya faru. Kamfanin ya kuma kara da cewa dakatar da fitar da man daga bututun zai taimaka wajen rage yawan illar da man dake malala zai yi wa muhalli, kuma tuni ya sanar da hukumomin da al'amarin ya shafa.

Hare-hare

A ranar Asabar din da ta gabata ne wata kungiyar masu fafutuka da makamai a yankin Naija Delta ta ce ta kai wasu hare-hare a kan wasu wuraren hada-hadar man fetur na kamfanin Chevron na kasar Amurka da kuma Agip na kasar Italiya a yankin na Naija Delta.

Kungiyar tana karkashin jagorancin John Togo ne, wanda a yanzu hukumomin sojin kasar a yanzu ke nema ruwa a jallo.

Hare-hare na baya-bayan nan da hukumomin soji suka kai a wasu kauyuka a kokarin kanme John Togo din ya janyo mutuwar wasu fararen hula.

Hukumomin sojin kasar sun ce sojoji takwas da kuma fararen hula shida ne suka mutu sakamakon hare-haren.

Sai dai an samu bambance-bambance a adadin mutanen da suka rasa rayukansu inda wasu kungiyoyi a yankin ke ikirarin cewa a kalla fararen hula tara aka kashe yayinda aka kona gidaje fiye da dari da hamsin a kauyen Ayakoromo.

Koma baya ga yawan mai da ake fitarwa

Najeriya dai ita ce kan gaba a nahiyar Afrika wajen arzikin da kuma hada-hadar danyen man fetur, sai dai hare-haren da masu tada kayar baya a yankin Naija Delta ke kaiwa bututun man da kuma wuraren hakar mai a yankin na kawo koma baya ga yawan man da take fitarwa don samun kudaden shiga a kasuwannin duniya.

Su dai masu fafutuka a yankin na Naija Delta sun ce suna kai hare-haren ne domin neman a yiwa yankin adalci a yadda ake rabon arzikin kasa da ake samu daga man fetur.

Sai dai masu sharhi a kan al'amura na ganin a yanzu ba za a iya banbancewa kai tsaye tsakanin masu fafutuka domin yankin ba da kuma masu kai hare-haren domin aikata laifuka.

Da dama daga cikin Jagororin kungiyoyin da ke kai hare-haren dai na azurta kansu daga kudaden da suke samu daga man da suke sata daga bututun da suke fasawa da kuma kudaden fansar da ake biyansu idan sun yi garkuwa da mutane musamman ma'aikatan kamfanonin mai na kasashen waje da ke aiki a yankin.

Hare-haren da kungiyoyin suka rika kaiwa a baya, ya kawo wa Najeriya koma baya a yawan man da take fitarwa, wanda a ya nzu ya daidaita a kan ganga miliyan biyu da dubu dari biyu a kowacce rana.