Korea ta Kudu za ta ci gaba da atisayenta

Sojojin Korea ta Kudu
Image caption Sojojin Korea ta Kudu

Duk da barazanar da Korea ta Arewa ta yi cewa za ta kai harin da ya fi wanda ta kai a baya muni, Korea ta Kudu ta tabbatar da cewa za ta kaddamar da atisayen sojinta kamar yadda aka tsara.

Shirin fara atisayen ya hada da umurni ga mazauna tsibirin Yeonpyong su shige wuraren fakewa daga harin bom.

Kafofin yada labarai na kasar ta Korea ta Kudu sun bayar da rahoton karuwar makaman harba rokoki na Korea ta Arewa a kusa da kan iyakar kasashen biyu.

Wannan mataki dai na zuwa ne a daidai lokacin da wani taron gaggawa na Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya don warware rashin jituwar da ke tsakanin kasashen na Korea a kan wannan batu ya tashi ba tare da cimma wata matsaya ba.

Bayan kwashe sama da sa'o'i takwas suna taron a asirce, mambobin Kwamitin sun kasa cimma matsaya ne a kan irin kalaman da ya dace a yi amfani da su.

Yayin da Rasha da China suka nemi a bukaci sassan biyu su yi taka-tsantsan, akasarin mambobin Kwamitin a karkashin jagorancin Amurka sun nemi a yi kakkausar suka a kan Korea ta Arewa, wadda suka zarga da tayar da wannan kura ta diflomasiyya.