Alamar sassauci daga Korea ta Arewa

Korea

Bisa dukkan alamu gwamnan jihar Texas ta Amurka, wanda ya kasance tamkar mai kai kawo tsakanin Amurka da Korea ta Arewa ya cinma wata yarjejeniya da hukumomin kasar.

Wata sanarwa da ofishinsa ya fitar ta yi marhabin da shawarar Korea ta Arewa ta daukia cewa ba zata maida martani ba ga atisayen soja na baya bayan nan da Koriya ta Kudu ta yi ba.

Hakan dai alamu ne dake nuna cewar gwamnatin koriya ta Arewa ta yi sassaucin matsayi, wanda hakan na iya sa a sake komawa shawarwari kan shirin nukiliyarta.