Nuri Al Maliki zai nada ministoci a Iraki

Firayim Ministan Iraki, Nouri al-Maliki
Image caption Firayim Ministan Iraki, Nouri al-Maliki

Nan ba da jimawa ba ne ake sa ran Firayim Ministan Iraki, Nouri al-Maliki, zai bayyana sunayen ministocinsa.

Zai yi hakan ne kuwa fiye da watanni tara bayan da aka gudanar da zabukan majalisar dokokin kasar da bai kammalu ba.

Akwai kusan mukamai arba’in da za a cike.

Zai kuma rarraba mukaman ne a tsakanin bangarorin kasar daban-daban.

Ana dai kallon kafa sabuwar gwamnatin a matsayin wani muhimmin ci gaba; sai dai babu wani abin da za a iya gani, har sai an rantsar da ministocin sun kuma kama aikin tunkarar matsalolin kasar.

An dai dauki lokaci mai tsawo ana jiran zuwan wannan rana, kuma akwai 'yan matsalolin da za a iya cin karo da su nan gaba.