An kara wa'adin sojojin Majalisar Dinkin Duniya a Cote D'voire

Dakarun kiyaye zaman lafiya a Cote D'voire

Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya amince da kara tsawon wa'adin dakarunsa dake kasar Cote D'voire da watanni shidda.

Wannan mataki wani babban kalubale ne ga Luarent Gbagbo, wanda ya ki rungumar kaddara na kayen da ya sha a zaben da akayi a kasar.

Tun da farko dai Mr Gbagbo ya umarci dakarun Majalisar da su fice da ga kasar.

Wakilin Majalisar Dinkin Duniya na musamman a Cote D'voire Mr Choi Young-jin yace, ba inda sojojin Majalisar zasu je.

Yace ''Wannan barazana ba zata hana dakarun Majalisar Dinkin Duniya gudanar da aikinsu ba, za su ci gaba da kasancewa a kasar a halin da ake ciki.

Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira ga Mr Gbagbo da ya mutunta zabin jama'ar kasar, ya sauka daga kan karagar mulki cikin ruwan sanyi, domin baiwa Mr Alassane Ouattara mulki, wanda aka yi amannar shine ya lashe zaben da aka yi a kasar.