Ba za'a yi mini adalci a Sweden ba - Assange

Image caption Julian Assange

Shugaban shafin nan mai kwarmato bayanai na Wikileaks, Julian Assange ya shaida wa BBC cewa zai yi duk mai yiwuwa domin hana tasa keyar sa zuwa kasar Sweden, saboda a cewarsa ba za a yi masa adalci ba a can.

Mista Assange ya bayanna hakan ne a wata hira da ya yi a wani shirin BBC, a gidan da yake zaune a gabashin Ingila.

Shugaban Wikileaks ya ce matan biyu da suka shigar da kara kan zargin ya yi musu fyade, suna cikin rudu ne.

Mista Assange ya musanta duk zargin da ake yi masa, inda ya ce ana amfani ne da karfin siyasa, domin cin zarafinsa.

An dai bada belin mista Assange mai shekarun haihuwa 39 a Burtaniya, kuma yana fuskantar karar neman tasa keyar sa zuwa Sweden.

Mista Assange ya shaida wa BBC cewar: "Bana bukatar in koma Sweden."

"Doka ta ce ina da 'yanci a matsayin dan adam, kuma duk mai zargi na da wani laifi ya gabatar da hujjojinsa ga kuliya a kowace kasa, amma ba sai an tasa keya ta wata kasa ba."