ECOWAS ta ce Gbagbo ya sauka cikin martaba

Image caption Laurent Gbagbo

Shugabannin kungiyar habbaka tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ta ECOWAS ko CEDEAO sun yi kira ga Laurent Gbagbo ya mika mulki cikin martaba ba tare da bata lokaci ba.

Wata sanarwa da ECOWAS ta fitar yau dinnan ta kuma gargadi Laurent Gbagbo akan cewar ya daina fito na fito da dakarun samar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya dake kasar.

Kiran na kungiyar ECOWAS ya zo ne yayinda ake ci gaba da ja-in-jar siyasa a kasar Ivory Coast, bayan zaben shugaban kasar da ake cewar jagoran 'yan adawa Alassane Ouattara ne ya lashe, amma Mr Gbagbo ya ce ba zai sauka ba.

Mai magana da yawun Alassane Ouattaran, mutumin da ake ganin shi ya lashe zaben shugaban kasar na Ivory Coast, yayi kira ga dakarun kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya da su kawar da shugaban kasar mai ci Laurent Gbagbo daga kan karagar mulki.

Mr Patrick Achi ya bayyana hakan, yana mai cewa matakin shi zai kawo karshen zub-da-jini, yayinda jayayyar neman iko ke ci gaba. .

Sai dai kuma gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa zata ci gaba da bin duk hanyoyin da suka kamata wajen ganin an kawo karshen rikicin siyasar daya barke a Ivory Coast, biyo bayan zaben shugaban kasar da ake ta takaddama akai.

Gwamnatin Najeriyar ta kuma ce rikicin siyasar Ivory Coast tamkar darasi ne ga sauran kasashen dake Nahiyar Afrika.

Ministan harkokin wajen Najeriya Dr. Aliyu Idi Hong , ya shaidawa BBC cewa cewa shugaban da Nigeria ta sani a Ivory Coast shine Allasane Oattara