INEC ta kafa Majalisar tuntubar juna ta tsaro

Image caption Shugaban Hukumar Zabe, Attahiru Jega

A Najeriya, hukumar zabe ta kasar ta kafa wata majalisar tuntubar juna ta jami'an tsaro domin shawo kan kalubalen da ta ce ta na fuskanta ta fuskar tsaro wurin gudanar da ingantaccen zabe a kasar.

A cewar hukumar, babban kalubalen da ke fuskantarta shi ne yadda hukumomin tsaro dabam-dabam ke kasa aiki a tare, abinda ke jawo kafafen da bata-gari ke iya amfani da su wurin dagula zaben kamar yadda aka sace na'urorin rajistar masu zabe guda ashirin.

Hukumar zaben Najeriya INEC ta ce ta kafa majalisar tuntubar junan ne tsakanin hukumomin tsaron kasar domin tabbatar da shigar jami'an tsaron cikin tsare-tsaren gudanar da zabe da kuma basu damar daukar matakan da suka dace da matsalolin da ake fuskanta a wuraren da aka turasu aiki maimakon yin tsari guda daya a fadin kasar da ba lallai ya yi aiki a wasu lunguna da sakunan Najeriyar ba.

Haka kuma hukumar na cewa hadin kan hukumomin tsaron zai taimaka wurin shawo kan kowace irin matsala.

Yanzu haka dai 'yan Najeriya sun zubawa hukumomin tsaron ido don ganin irin rawar da za su taka wurin tabbatar da ingantaccen zabe a kasar.