Rahoton Amurka ya ce an saki Al-Megrahi bisa dalilai na siyasa ne

Wani rahoton Amurka, a kan shawarar da gwamnatin Scotland ta yanke, ta sakin dan Libiyar nan da aka samu da hannu a harin jirgin saman Lockerbie, ya ce an sake shi ne saboda dalilai na siyasa.

A watan Ogustan bara ne aka saki Abdelbaset al-Megrahi daga gidan kurkuku, bayan da gwamnatin Scotland ta ce watanni ukku kawai suka rage masa a duniya, saboda cutar kansar da yake fama da ita.

Sai dai kuma rahotan wanda sanatocin Amurka hudu ke marawa baya, ya ce ba wani binciken kimiyyaa da ke nuna hasashen da suka yi.

Haka kuma rahoton ya ce a lokacin da aka sake shi , Birtaniya ta ji tsoron rasa Dala miliyan 900 na hakar mai ta hannun Kamfanin mai na Birtaniya -BP.

Gwamnatin yankin Scotland dai ta yin watsi da daukacin rahoton.

An dai samu Al-Megrahi da laifin tarwatsa wani jirgin saman fasinjan Amurka a saman sararin samaniyar garin Lockerbie a cikin watan Disamban shekarar alif dari tara da tamanin da tkwas, abinda ya halaka mutane 270.