Gyaran dokar zaben Najeriya

Harabar majalisar dokokin Najeriya
Image caption An kammala aiki kan gyaran dokar zabe

A Najeriya, a daren jiya ne kwamitin hadin gwiwa na Majalisun Dokokin kasar ya yi zama na musamman domin shawo kan rarrabuwar kawunan da ke tsakanin Majalisun biyu, game da kundin dokar zabe ta bana.

Hakan dai ya biyo bayan amincewar da Majalisun biyu suka yi da dokar a lokuta daban-daban.

Wannan doka dai ita ce za ta ba da damar gudanar da zabukan shekara ta 2011.

Sanata Ahmed Lawan na daga cikin 'yan kwamatin hadin gwiwar, ya shaidawa BBC cewa sun kammala aiki kan dokokin zaben kuma za su gabatarwa majalisa don amincewarta.

Ya kara da cewa bayan mikawa majalisa gyare-gyaren da suka amince da su ne za a bayyanawa jama'a cikakken abin da kundin ya kunsa.