Bikin sauyin mulki a Guinea

Alpha Conde
Image caption Alpha Conde zai yi rantsuwar kama aiki

Idan an jima a yau ne za a rantsar da shugban farar hula na farko a kasar Guinea, Alpha Conde a bikin da ake ganin zai samun halartar da dama daga cikin shugabannin kasashen Afirka.

Mista Conde, wanda tsohon dan siyasar adawa ne, ya sha alwashin magance matsalolin da tashen-tashen hankula na kalibilanci da kuma siyasa suka haifar a kasar.

A watan jiya ne dai, Mr Conde ya samun nasara a zaben shugabancin kasar Guinea na farko tun bayan da kasar ta samu 'yanci kai a shekarar 1958, da kuri'u hamsin da uku cikin dari.

Masu nazari na kallon wannan sauyi na siyasa a matsayin wata hanya ta magance rikice-rikicen da aka yi fama da su a kasar.