Ecowas ta kira taron gaggawa akan Cote D'voire

Ecowas

Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Afrika ta Yamma, ECOWAS ko CEDEAO ta ce shugabanninta zasu gudanar da wani taron gaggawa jibi Juma'a a Abuja, Nijeriya, kan kasar Cote D'voire, wadda ke fama da takaddamar siyasa.

Tun a kwanakin baya kungiyar ta bada sanarwar dakatar da kasar Kotde vuwa, bayan da shugaban kasar mai ci yanzu, Laurent Gbagbo ya ki sauka daga kan mulki, duk da sakamakon zaben dake nuna cewar jagoran 'yan adawa Alassane Ouattara ne ya lashe zaben shugaban kasar na makonnin baya.

Sanarwar da kungiyar ta ECOWAS ta fitar ta kara yin kira ga Laurent Gbagbo da ya sauka, ya kuma mika mulki ga Alassane Ouattara. Daga Abuja ga karin bayanin da Aliyu Abdullahi Tanko ya aiko mana;