Rikicin Burtaniya da Rasha

Fira Ministan Burtaniya, David Cameron
Image caption Rikicin difilomasiyya tsakanin Burtaniya da Rasha

Kasashen Burtaniya da Rasha sun kori jami'an difilomasiyyar juna bisa zargin leken asiri.

Ofishin harkokin wajen Burtaniya da ke Landan ya tabbatar da cewa a farkon watan Disemba, ya umurci wani jami'i a ofishin jakadancin Rasha da ya bar kasar, saboda ya rika gudanar da binciken da ya sabawa ka'idojin Burtaniya. Sai dai hukumomin kasar ba su ba da cikakken bayani kan zargin leken asirin ba .

Kwanaki shida bayan haka, Rasha ta sanar da korar wani jami'in difilomasiyyar Burtaniyar daga Birnin Moscow.