Faransa ta bukaci 'yan kasar ta da su fice daga Ivory Coast

Image caption Sojoji kiyaye zaman lafiya a Ivory Coast

Faransa ta bukaci 'yan kasar ta da su bar Ivory Coast cikin gaggawa, saboda rashin tabbas din rikicin siyasa a kasar.

Mai magana da yawun gwamnatin kasar Francois Baroin ya ce kasar ta dau matakin ne saboda kare rayuwar al'ummar ta.

Akwai akalla 'yan kasar faransa dubu 15,000 da ke zaune a kasar Ivory Coast.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki-moon ya yi gargadin cewa, kasar za ta iya shiga yakin basasa, kuma Laurent Gbagbo yana kokarin korar jami'an tabbatar da zaman lafiya na majalisar dinkin duniya daga kasar.

Kasashen duniya dai sun bayyana abokin takarar Gbagbo, Alassane Ouattara a matsayin wanda ya lashe zaben.

Majalisar dinkin duniya ta zargi shugaban kasar Ivory Coast Laurent Gbagbo da hayar 'yan bindiga wadanda za su taimaka masa wajen yakar jami'anta da ke kasar.