Laurent Gbagbo ya yi hayar 'yan bindiga

Babban sakataren majalisar dinkin duniya, Ban Kii Moon

Majalisar dinkin duniya ta zargi shugaban kasar Ivory Coast Laurent Gbagbo da hayar 'yan bidiga wadanda za su taikama masa wajen yakar jami'anta da ke kasar.

Babban sakataren majalisar, Mista Ban Ki-Moon ya kuma zargi Mista Gbagbo, mutumin da aka yi ammana shi ne ya sha kaye a zaben shugaban kasar da aka gudanar a kasar, da kokarin jefa kasar cikin yakin basasa.

Mista Ban ya ce Gbagbo ya yi hayar 'yan bindigar ne daga kasar Liberia.

Ya ce bangaren Mista Gbagbo na kokarin kawo cikas ga aikin dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar, wadanda ke kai kayayyaki ga mutane da ke bukatarsu.

Sai dai a jawabin da ya yi ga kasar, Mista Gbagbo ya musanta zargin.

Ya yi kira ga 'yan adawa su tattauna da shi don samun mafita ga rikicin siyasar da ya gallabi kasar.

Amma Alasanne Ouattara, wanda ya lashe zaben, ya ce Mista Gbagbo ba shi da niyyar sasantawa da 'yan kasar tun da ya ki amince da shan kaye.