Ma'aikatan sufuri na yajin aiki a Girka

Jami'an 'yan sanda a Girka
Image caption 'Yan sanda sun yi artabu da jama'a a baya a kan wannan batu na tsuke bakin aljihu

Wani yajin aiki da ma'aikatan sufuri ke yi a kasar Girka ya tsaida harkoki cik, a Athens, babban birnin kasar.

An shirya yajin aikin ne don ya zo daidai da lokacinda za a kada wata kuri'a a Majalisar Dokokin kasar, a kan kasafin kudin shekara mai kamawa ta 2011, kasafin da gwamnati ta shirya tsuke bakin aljihunta.

Ana sanya ran gwamnatin za ta samu nasarar amincewa da kasafin kudin, wanda aka shirya shi domin ya gamsar da hukumar bada lamuni ta duniya, IMF, da kuma Tarayyar Turai, a matsayin wani sharadi na baiwa kasar ta Girka lamunin dala biliyan 145.

Mazauna Athens dai sun duru cikin motocinsu domin tafiya aiki abinda ya haddasa mummunan cunkoson ababen hawa akan hanyoyin da suka nufi tsakiyar birnin.

Rashin gamsuwa

Ma'aikatan sufurin dai sun shiga yajin aikin ne domin bayyana rashin gamsuwa da shirin gwamnati na rage musu albashi kamar yadda kasashenda ke bin Girka bashi suka bukata.

Kasafin kudin na shekarar 2011 ya hada da karin harajin sayen kayayyaki da rage kudaden da ake kashewa kiwon lafiya da kamfanoni mallakar gwamnati da ma bangaren tsaron kasa.

Ana dai samun karin rabuwar kai tsakanin 'yan Majalisar jam'iyyar gurguzun da ke mulkin kasar.

Wata 'yar jam'iyyar da ke da tasiri a majalisar duk da dai ba ta da mukami a gwamnati, Vasso Papandreou, wadda tsohuwar kwamishina ce a tarayyar Turai, ta ce kasafin ba zai iya ceto Girka daga halin karayar tattalin arzikin da ta shiga ba.

Jam'iyyar firaministan dai na da rinjaye a majalisar da kujeru shida kuma ana sa ran dokar kasafin kudin za ta yi nasara.