Matatun mai uku a Najeriya sun tsaya cik- NNPC

Babban Kamfanin mai a Najeriya - NNPC ya ce matatun mai uku cikin hudu da kasar ke da su sun tsaya cik, saboda harin da masu fafutuka su ka kaiwa wasu daga cikin bututun man kasar.

Kamfanin na NNPC ya ce lallata bututun mai din, ya sa ayyuka a matatun mai a Warri da Kaduna da kuma Port Harcourt sun tsaya, a yayin da kamfanin ya ki ya bayyana adadin kwanakin da matatun za su yi ba sa aiki.

Najeriya dai na shigowa ne da kashi 85 cikin dari na bukatun man da take amfani da shi daga kasashen wajen, kuma rufe matatun man zai sa man da kasar ke amfani da shi ya ragu da ganga 445,000 a kowacce rana.

Kamfanin na NNPC ya ce babban darektanta ya gana da hafsan sojan kasa a ranar Talata domin neman kariya ga batutunta da ke Bonny da kuma Escravos.

A wannan makon ne ma kamfanin mai na Chevron ya ce ya dakatar da fitar da mai daga Najeriya, saboda an lallata masa wasu daga cikin bututun da yake fitar da man.