Obama ya hana baiwa Congo tallafi

Shugaban Amurka, Barack Obama
Image caption Obama ya hana baiwa Congo tallafi

Shugaban Amurka Barack Obama ya sa a hana baiwa jamhuriyar dimokaradiyyar Congo tallafin kasuwanci, inda ya ce hakan hanya ce ta tabbatar da shugabanci nagari a Afirka.

A wata sanarwa da ya fitar, shugaba Obama ya ce ya hana baiwa kasar tallafi ne saboda ba ta samu ci gaban da kasashen duniya suke bukatar ta yi ba.

A duk shekara gwamnatin Amurka tana yin nazari kan tallafin kasuwancin da ta ke baiwa kasashen Afirka ta hanyar barin su shigowa da wasu kayayyaki ba tare da sun biya haraji ba.

Kasar Congo dai ta yi fama da yake-yake, abin da ya kawo koma-baya ga ci gabanta.