An kori 'yan sanda 3 akan laifin fyade a Kano

'Yan sandan Nigeria
Image caption 'Yan sandan Nigeria

Rundunar 'yan sandan jahar Kano a Nigeria ta kori wasu 'yan sanda biyu daga bakin aiki bisa samunsu da laifin yiwa wata yarinya fyade.

Haka nan kuma rundunar 'yan sandan ta ragewa wani mukami akan wannan laifi yayin da ta ce ta na cikin farauratar wasu farar hulla da ke da hannu a fyaden.

Rahotanni sunce 'yan sandan sun yi garkuwa da yarinyar 'yar shekaru 16 inda suka yi ta yi mata fyade har tsawon kwanaki 28, tare kuma da karbar kudi daga wasu fararen hula domin yin amfani da yarinyar.

Lamarin dai ya ja hankalin kungiyoyin kare hakkin bil adama da na lauyoyi, inda suka yi kiran a dauki mataki akan wadanda suka aikata wannan laifi.

Dama dai yan sanda uku ne ake zargi da aikata laifin, sai kuma fararen hula uku wadanda akace yanzu haka sun gudu.