Majalisar Amurka ta amince da yarjejeniya kan makaman nukiliya

Majalisar dokokin Amurka

'Yan Majalisar dattawan Amurka sun amince da yarjejeniyar da Amurka ta kulla da Rasha kan rage yawan makaman nukiliyarsu.

Yarjejeniyar wacce aka yiwa lakabi da New Start za ta sa kasashen su rage makaman nukiya da kashi uku bisa dari, sannan su janye jiragen ruwansu wadanda ke dauke da makaman nukiliya a karkashin teku.

Wasu 'yan jam'iyyar adawa ta Republicans sun soki yarjejeniyar, inda suka ce an tsara ta ne don cimma wani burin siyasa.

A watan Afrilun da ya gabata ne kasashen Amurka da Rasha suka sanya hannu kan yarjejeniyar, kuma amincewa da ita wata galabar siyasa ce ga shugaban Amurka Barack Obama.