Koriya ta Kudu ta fara atisaye

Sojojin kasar Koriya ta Kudu

Rundunar sojin Koriya ta Kudu sun fara atisaye kusa da iyakar kasar da Koriya ta Arewa a lokacin da ake ci gaba da zaman zulumi a yankin.

Koriyan za ta yi amfani da tankoki, da jiragen sama masu saukar-ungula, da kuma jiragen saman soji a atisayen da za ta yi a yankin Pocheon mai nisan kilomita talatin daga iyakarta da Koriya ta Arewa.

A watan daya jiya dai wani harin da Koriya ta Arewa ta kaiwa Koriya ta Kudu ya yi sanadiyar mutuwar mutane hudu.

Amurka na goyon bayan Koriya ta Kudun kan atisayen da take gudanarwa.