An rasa rayuka a hadarin mota a Bauchi

Rahotanni daga jihar Bauchi a tarayyar Nijeriya na cewa Mutane goma sun rasa rayukansu, wasau Karin goma kuma sun sami munanan raunuka a wani mummunan hadarin mota a kan hanyar Darozo, kusa da garin na Bauchi.

Daya daga cikin motoci biyu da suka yi hadarin dai ta rufta a cikin wani kwalbati ne, dama kuma suna kan han yarsu ce daga Yobe zuwa garin Bauchi domin halartar ziyarar da shugaban Nijeriya Dokta Goodluck Jonathan ya kai a Bauchin yau, a cigaba da yakin neman zabensa.

Wadanda hadarin ya rutsa da su dai 'yan kungiyar kade-kade da raye-raye na al'adun gargajiya ne, kuma galibinsu sun kone kurmus.