EFCC na bincikar Amos Adamu

Hukumar EFCC na bincikar Amos Adamu na hukumar kwallon kafa ta duniya
Image caption Amos Adamu

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon-kasa a Nigeria, EFCC, ta ce ta fara gudanar da binciken da ya shafi cin hanci da rashawa, a kan dan kwamitin zartarwar hukumar kwallon kafa ta duniya wanda aka dakatar, Mr Amos Adamu.

Daya daga cikin abubuwan da Hukumar ta ce tana bincikensa a kansu shi ne yadda aka kashe tsabar kudi naira bilyan ashirin da hudu a kan wasannin COJA da aka yi a Najeriyar, lokacin da ya shugabanci kwamitin shirya wasannin a shekara ta 2003.

A jiya ne dai hukumar EFCC ta gayyaci Mr Amos Adamu zuwa hedikwatarta a Abuja domin ya amsa tambayoyi.