Tattaunawa kan rikicin Ivory Coast

Taswirar kasar Ivory Coast
Image caption Ana tattaunawa kan rikicin Ivory Coast

Amurka ta ce tana tattanaunawa da Faransa don samun mafita kan rikicin siyasar kasar Ivory Coast.

Kakakin ma'aikatar harkokin kasashen wajen kasar P.J. Crowley, ya ce Amurka ta damu sosai kan rikicin don haka za ta yi kokarin ganin an magance shi.

Ya kara da cewa tattunawarsu da Faransar za ta basu damar bullowa lamarin cikin hikima.

Ita ma Majalisar Dinkin Duniya a yau Alhamis za ta gudanar da taron gaggawa kan rikicin siyasar na Ivory Coast.

Taron, wanda Najeriya da Amurka suka kira, na zuwa ne bayan matsin lambar da shugaban da ya ki amincewa da shan kaye, Laurent Gabgbo ya fuskanta daga kasashen duniya don ganin ya sauka daga mukaminsa.

Ranar Laraba dai, Alasanne Ouattara, ya ce yin amfani da karfin soji don kawar da Mr Gbagbo ita ce hanyar da za ta wanzar da zaman lafiya a kasar.