Majalisar dattawa zata hana kashe kudi

A Najeriya majalisar dattijan kasar ta ce ba zata amince da kasafin kudin duk wata ma'aikatar gwamnati da ba ta gurfana gabanta, tare da bayanai dalla dalla akan yadda zata kashe kudi a badi ba.

Hakan dai na nufin cewar ma'aikatu kamar su Babban Bankin Najeriya , CBN, da hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa wato NPA da makamantansu duk sai majalisar ta amince da kasafin kudinsu kafin su gudanar da ayyukansu a badi, sabanin yadda ake yi a baya.

Wannan matakin na majalisar dattijan na zuwa ne makonni kadan da shugaban babban bankin, Sanusi Lamido Sanusi ya bayyana cewar kudaden gudanarwa da ake kashewa a majalisun kasar sun wuce kima.