kungiyar ecowas na taro kan ivory coast

ECOWAS/CEDEAO
Image caption Tambarin Ecowas ko Cedeao

Shugabannin kasashen Afrika ta yamma suna gudanar da wani taro domin tattauna yadda al'amura ke tafiya a Cote d Ivoire bayan zaben shugaban kasar da ake takaddama akai.

Kakakin kungiyar ya bayyana cewa wannan taro da ake yi a Nijeriya zai tattauna abu guda ne kawai, wato yadda za a sauya mulki a Cote d Ivoire zuwa ga mutumin da kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Afrika ta Yamma wato Ecowas, da majalisar dinkin duniya suka amince da shi a matsayin wanda ya lashe zaben, wato Alassane Ouatara.

Wani taron makamancin wannan a baya ya bukaci shugaba Laurent Gbagbo da ya gaggauta sauka daga kan mulki, tun da ba shi ne yayi nasara a zaben ba.