Ecowas za ta yi amfani da karfi kan Gbagbo

Ivory coast
Image caption Sojojin Majalisar Dinkin Duniya ne ke bai wa Ouattara kariya

Shugabannin kungiyar Ecowas sun kara kira ga Laurent Gbagbo da ya sauka daga shugabancin Ivory Coast nan take, ko kuma a hambarar da shi da karfi da yaji.

Kungiyar ta kuma yanke shawarar tura wata tawaga ta musamman zuwa kasar Ivory Coast, don baiwa Laurent Gbagbo dama ta karshe na ya sauka daga karagar mulkin.

A karshen taron gaggawa da suka kammmala da a ranar Juma'a a Abuja, shugabannin sun ce nan bada jimawa bane manyan hafsoshin sojojin kasashen dake kungiyar, za su tattauna don tsara hanyoyin da za'a bi wajen hambararda Laurent Gbagbo matukar ya yi kunnen kashi.

Kungiyar ta kuma ce tana goyon bayan duk matakan da kasashen duniya suka dauka na takunkumin hana tafiye-tafiye da kuma tattalin azriki kan Mr Gbagbo dana kusa da shi.