Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Tarihin zuwan Hausawa kasar Kamaru

Image caption Husawa sun shafe fiye da shekaru dari a kasar Kamaru

Tarin litattafan tarihin da aka rubuta a kan kafuwar al'ummomi a Kamaru sun bayyana cewa shigowarsu ya gudana ne daki-daki daga inda suka taso.

Dalilai da dama ne kuma suka dinga shigowa da su ko da yake mafi muhimmanci shi ne kasuwanci da kuma yin musayar kayan haja tsakaninsu.

Hakan kuma ya fara tun gabanin shigowar Turawan mulkin mallaka na farko wato Jamusawa, wadanda bayan shigowarsu Kamaru a shekara ta 1884 suka fada cikin harkokin kwadago tare da jama'ar da suka tarar a sarari.

Hausawa wadanda suma suna kafe a duk sassan Kamaru na daga cikin wadanda suka yi kaura daga matsuguninsu na asali izuwa inda a yau suke zaune sama da shekara 100.

A dalilin haka ne Mohaman Babalala ya hada mana rahoto na musamman a kan dalilan da suka shigo da hausawan Foumban da kuma na Kumba hadi da irin sana'o'in da suka runguma.