Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Yadda za a magance rikicin addini da kabilanci a Afrika

Image caption Sojoji suna sunturi a garin Jos na tsakiyar Najeriya

Wani batu da Afrika ta yi kaurin suna a kai a 'yan shekarun nan shi ne na rikice-rikicen da take fama da su ko dai na addini ko kabilanci, wadanda a wasu lokuta ke haddasa asarar dimbin rayika.

Domin daidaita al'ammura, yanzu haka wasu kungiyoyin addinai sun tashi tsayin daka da nufin samar da kyakyawar dangantaka tsakanin addinai da kabilu a Afrika ta yadda nahiyar za ta samu ci gaba mai dorewa.

Daya daga cikin irin wadannan kungiyoyi, ita ce Cibiyar samar da kyakkyawar fahimta tsakanin addinai dake Kaduna a Nijeria.

Kungiyar dai ta taimaka wajen samar da zaman lafiya a Kenya, sakamakon takaddamar da ta biyo bayan zaben shugaban kasa a shekara ta 2008.

Kungiyar ta yi imanin cewa 'yan Afrika da kansu ne za su iya magance matsalolin da suke fuskanta.

Imam Mohammed Nurain Ashafa da Pastor James Wuye su ne shugabannin wannan Cibiya, kuma a kwanan baya sun ziyarci Ofishinmu na London inda Elhadji Diori Coulibaly ya tattauna da su, kamar yadda za ku ji a wannan hirar.