Isra'ila ce ta kai hari a Syria a 2007

Wani rahoto daga jaridar kasar Isra'ila, Yedioth Ahronoth, ya yi bayani wani sako na diflomasiya da ba a wallafa ba zuwa yanzu daga taskar bayanai ta Wikileaks, wanda ya tabbatar da cewa Isra'ila ta kai harin bom a tashar nukiliya ta Syria a shekara ta 2007.

Sakon, wanda tsohuwar Sakatariyar Waje ta Amurka, Condoleezza Rice ga ofisoshin jakadancinta na kasashen waje, ya yi bayanin dalilan Isra'ila na kai harin.

Kasar Syria dai ta sha musanta cewar ginin da aka ruguza din tashar nukiliya ce.