Makamai:Kotu ta bayar da belin dan Iran

Wasu daga makaman da aka kama a Najeriya

Wata Kotu a Najeriya ta bayar da belin dan kasar Iran din nan wanda ake zargin da hannu wajen shigowa da makamai ta haramtacciyar hanya cikin kasar.

Kotun ta bayyana Azim Aghajani a matasyin dan kasuwa, kuma mamba a hukumar tsaro da juyin juya-hali ta kasar Iran.

An dai gurfarnar da Mista Azim tare da wasu 'yan Najeriya su uku a gaban kuliya ne bayan da aka gano wani jirgin ruwa da ke dauke da rokoki, da gurneti, da kuma bindigogin igwa a wata tashar jirgin ruwa da ke Lagos a watan Oktoban da ya gabata.

Kama makaman ya kawo zazzafar mahawara a kasar, kana ya janyo hankalin kasashen duniya.