Najeriya za ta karbo bashi

Taswirar Najeriya
Image caption Najeriya za ta karbo bashi

Ma'aikatar kudin Najeriya ta ce gwamnatin kasar za ta karbo bashi na kusan dala biliyan daya daga bankin Eximbank na kasar China domin samar da abubuwan more rayuwa a kasar.

Najeriya za ta karbi bashin ne duk da damuwar da babban bankin kasar ya nuna, kan yawan bashin da kasar ke karbowa daga kasashen waje, da kuma yawan kudaden da gwamnatin kasar ke kashewa.

Ana dai sa ran cewa gibin kasafin kudin kasar zai kai kashi shida cikin dari a shekarar da muke ciki, kuma adadin kudin kasar da ke ajiye a kasashen waje ya ragu da kashi ashirin cikin dari a bara.

Najeriya dai na daga cikin kasashen da ke fitar da danyan mai, kuma tana samun akasarin kudaden shigarta ne daga man da ta sayar.