Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Shirye-shiryen zaben shugaban kasa a Nijar

Image caption Shugabannin mulkin sojin Nijar sun sha alwashin mika mulki ga farar hula

A jamhuriyar Niger yayin da ake ci gaba da shirye-shiryen zabukan shekara ta 2001, wani batu da ke jan hankalin jama'ar kasar, shi ne cewa galibi 'yan takarar da suka sabawa tsayawa ne, jam'iyyunsu su ka sake tsayar wa a wannan karon ma.

Wannan al'ammari dai ya sa jama'a na tafka muharawa inda wasu ke ganin cewa wannan wata alama ce ta rashin Dimokradiyya a cikin jam'iyyun.

Yayin da wasu kuwa ke cewa lokaci ya yi da jam'iyyun za su ba sabbin jini damar nuna kamun ludayin su.

Sai dai magoya bayan 'yan takarar suna cewa ai ma'anar Dimokradiyya shi ne zabin jama'a.

Ya zuwa yanzu dai 'yan takara goma ne Hukumar zabe ta amince da takararsu ta neman mukamin shugaban kasa a zaben na badi.

Wakilin mu a Yamai Idy Barau ya duba wannan batu, ga kuma rahoto na musamman da ya shirya mana: