Bikin kirsimeti a Jamhuriyar Nijar

A shekara ta 2010 alkaluma na nuna cewa, yawan al'umar Nijar sun haura sama da miliyan 15, daga cikinsu fiye da kashi 98 cikin 100 na bin addinin musulunci ne yayinda mabiya addinin kirista ba su kai kashi 2 a cikin 100 ba.

Pasto Sama'ila Labo na majami'ar unguwar Bukoki a birnin yamai a wata hira da ya yi da BBC, ya tabbatar da cewa ana samun kirista a cikin daukacin jahohi da kabilun Nijar

"Hakikan kiristanci na ci gaba da yaduwa, wannan kuwa bisa ga alkawali wanda Allah ya yi cewa kwanaki na karshe zan aiko muku da ruhuna domin ya sanar da magana ta a cikin zukatan mutane. Saboda haka wannan jawabi na kiristanci yana watsuwa kuma mutane da yawa suna karbarshi."

"Idan na dauka tun daga nan Yamai, akwai kiristoci wadanda yan nijar ne uwa da uba, Doso, Dogon Dutsi,Konni,Galmi akwai eglisiyoyi. Yankin Maradi za mu iya cewa shi ne inda kiristoci suka fi yawa,Dogon Dutsi ma yanki ne inda ke akwai kirista da dama."

Sallolin Kirista

Kiristan dai na da bukukuwa da dama, daga cikinsu akwai Noel ko kirismeti wadda suke tafiyar da shagulgulanta na kowace shekara a ranar 25 ga watan Disamba domin tunawa da ranar haihuwar annabi Isa alaihis salam.

Wasu mabiya addinin kiristan da BBC ta samu a wuraren ibadarsu cikin birnin Yamai, sun yi karin haske a kan ma'anar wannan bikin.

"Salla ce wadda ke ba mu damar mu tuna da haihuwar almasihu Yesu wanda shike ubangijin ban gaskiyarmu mai cetonmu kuma".

"Albarkacin wannan salla muna hidimomi,muna murna kamar yadda dai salla take mai ibada wadda za ta kawo daukaka da daraja ga ubangijin da muke bauta wa."

Sakon Kirsimeti

Shi ko wannan cewa ya yi : "A gani na salla ce da take ba kowane kirista damar tunawa da haihuwar Isa mai ceto wanda Allah ya yi wa alherin dukan duniya."

Ita ko wata mata cewa ta yi: "Salla ce wadda ake yi tare da iyaye ana nuna murna ga haihuwar mai ceto. A da duniya cike da zunubi take sai Allah ya ga zunubi ya yi yawa sai ya aiko Yesu ya wanke mana zunubbanmu."

A shekarar bana babban filin wasanni na birnin Yamai ne hadin gwiwar majami'o'in Yaman suka taru ranar Lahadi 19 ga watan Dsamba. Makada da mawaka suka cashe, yayinda wasu pastoci suka yi wa'azi.

Fasto Hasan Dan Karami shi ne shugaban hadin gwuiwar kungiyoyin mabiya addinin kiristan nijar, ya kuma yi karin bayani a kan dalilinsu na zaben ranar 19 ga watan na Disamba domin gudanar da shagulgulan.

"Wannan rana ta kasance rana ce ta musamman saboda yau shekara 50 da muka samu mulkin kai."

"Cikin maganar Allah shekara 50 shekara ce ta samun yanci da nasara, shi ne za mu zo mu yi addu'a mu ce kasarmu bayan shekara 50 za ta sake sabon salo, za ta tashi da nasara kuma za mu ci gaba." In ji Fasto Dan Karami.

Ya kuma kara da cewa: "Mun zabi ranar 19 ga watan Disamba saboda sallar zama jamhuriya da muka yi ran 18 ga wata, bayan haka muna son mu ba sauran damar su yi salla ranar 24 wajajensu."

Ita ma shugabar mata mabiya addinin kiristan Mme Ibrahim Fati ta kara da cewa: "Ban san ba misalin da zan fadi domin in nuna murna ta da farin ciki domin wannan ranar. Tun shekaranjiya juma'a muka fara, mun hadu mu yi sujjada dukan kabilun Nijar an hadu mu 'yan kasa kirista don mu nuna farin cikinmu ."

Murna da ranar

A ranar ta 25 ga watan disamba, kiristoci na kasancewa cikin majami'ar su domin raya ranar da addu'o'i.

Pasto Sama'ila Labo na daga cikin manya manyan masu wa'azin addinin kirista:

" A matsayinmu na 'yan Nijar, ya kamata mu yi murna mu yi farin ciki mu shaida godiyarmu ga Allah sannan mu yi addu'o'i saboda shekaru wadanda muke da su a gabanmu, domin mun sani kasarmu tana da makoma wadda muke bukatar mu damka wa ubangiji A bangaren mata da matasa, banda ibada sukan shirya wasanni iri iri da kyaututuka.

Mme Cima Umaru na daga cikin shugabannin mata kiristar; "Wakoki ne za mu yi na yabon Ubangiji. Mun gayyato abokanmu su zo su ma su ji dalilin murnar mu."

" In kana jin dadi ka sa makwabcinka shi ma ya ji dadi." In ji Cima Umaru.

A gefe daya kuma, domin kara wa sallar ta bana armashi, matan sun gayyato wata mata mai suna Mama Agnes Tatan daga jihar Adamawa a Najeriya wadda ta shahara wajen tsara wakokin kira ga salama; "Cikin wakokin da nike yi akwai wakoki na karfafawa, akwai wakoki na bada shawara, akwai wakoki na kiran jama'a zuwa ga ceto, wasu kalmomin kuma na zaman salama ne ga iyali a cikin gidaje."

Ayyukan jin kai

Har ila yau bayan ibada da wasannin shakatawa, albarkacin wannan sallar kiristan kan yi wasu ayyuka na jinkai.

A bangaren dattijai, su kuma ko me suka fi mayar da hankali a kai lokacin sallar ta kirismeti? Ga abin da pasto Abdu Galadima ke cewa;

"To abin da muka fi ba karfi shi ne mu karfafa kanmu, da 'ya'yanmu, da mutane da suke jin mu."

"Duk mutumin da ka gani, in dai ya girma kuma yana da hankalinsa, abin da yake tunawa wai menene gobe na? Saboda haka muna son mutane su shirya gobensu tun yanzu."

A kasar ta Nijar dai kotun tsarin mulki da sauran dokoki na kasa sun ba duk wanda ke zaune a kasar damar yin addinin da yake so ba tare da wani ya takura masa ba.

Zamantakewa tsakanin Kirista da Musulmi

Saboda haka bayanai na nuni da cewa zamantakewa tsakanin kirista da musulmi na tafiya da kyau ya zuwa yanzu.

"Ni suna na Abbas Abdullahi, a cikin gidanmu ni kadai ne kirista, a yanzu haka babana limamin masallaci ne, amma kuma tsakanina da shi huldarmu tana tafiya da kyau, sauran 'yan uwana ma ba ni da wata matsala da su."

A albarkacin sallolin musulmi, shugaban mabiya addinin kirista Monseigneur Michel Kartateguy kan isar da sakon barka da salla ga musulmin ta kafofin yada labarai, tare da fatan Allah ya kara tabbatar da zaman lafiya tsakanin musulmin da kirista.

Haka zalika su ma musulmin sukan taya kiristocin murna. Sheik Cissé Amadou wakilin kungiyar addinin musulunci ta Nijar AIN, ya halarci bukukuwan na kirismeti; "Musulmi sun fi yawa a nijar amma yau mun gode wa Allah da ya sa mu zama uwa daya uba daya, babu matsalar da ke bullowa tsakaninmu da kirista. Musulmai na da hankali kiristan ma na da hankali."

"Duk wasu maganganun da za mu yi suna tsayawa ne ga baki, muna rokon Allah ya kara hada kai tsakaninmu." In ji Sheikh Cise.

Sakon kirsimeti

Daga bangaren gwamnati dai, bikin ya samu halartar mashawarcin shugaban kasa a fannin harkokin addini da darektan harkokin addinai a ofishin ministan cikin gida Malam Abdou Samadou Yahaya wand ya ce:

"Sakon da ke gare mu da sunan minister na cikin gida shi ne mu yi ma almasihun Nijar barka kuma muna jin dadin huldar da ke akwai tsakaninsu, rayuwa na tafiya daidai".

Game da tashe tashen hankulan da ke faruwa a kasashen duniya, albarkacin wannan salla, kiristan Nijar na addu'ar Allah ya kawo zaman lafiya a ko'ina.

"Koyarwa ta bayyana mana cewa in hali ya yi ku yi zaman lafiya da kowa da kowa. Kirista ya kamata a ko'ina kamar a Jos a Najeriya, Aljeriya Egypt, Sudan da kasashe kamar su Pakistan, muna bukatar mu karfafa zaman lafiya." In ji Pasto Sama'ila Labo.

Mabiya addinin kiristan na ci gaba da hidimomi iri-iri har zuwa ranar 31 ga watan Disamba, jajibirin sallar sabuwar shekara.

Wasu manya-manyan shaguna tuni suka sha ado, har ma wasu sun karya farashin wasu kayayyaki domin ba kowa damar tafiyar da sallar lami lafiya.