Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Al'ummomin kan iyakoki na fuskantar matsalolin rayuwa.

Image caption Taswirar Najeriya

Al'ummomin dake zaune a kan iyakoki musamman a kasashe masu tasowa galibi kan fuskanci matsalolin rayuwa fiye da kima inda za ka ga ba kasafai su kan samu kyakkawar kulawa daga hukumominsu ba.

A Najeriya dai irin wadannan al'ummomi sun dade suna fama da matsaloli kamar na tsaro,harkokin yau da kullum da rashin ababan more rayuwa.

Jihar Borno ita ce jihar da ta yi iyaka da kasashe uku, watau Nijar da Kamaru da Chadi, kuma al'ummomin jihar da dama ne ke zaune a yankunan kan iyakokin.

Da ma dai masu lura da al'ammura sun yi gargadin cewa kasashe 'yan kalilan ne a Afrika, ake ganin za su iya cimma muradun nan na karni, wadanda majalisar dinkin duniya ta waare, kan batun rage tallauci da kyautata kiwon lafiya da harkar ilimi nan da shekara ta 2015.