Dalibai sun fadi jarabawar waec warwas.

Yanzu haka mutane a Nijeriya na ci gaba da nuna damuwa dangane da faduwar da dalibai suka yi a jarrabawar Sakandare da Hukumar Shirya Jarabawa ta Afirka ta Yamma wato WAEC, ta gudanar a watannin Nuwamba da Disamban bana.

Sakamakon dai ya nuna cewa kashi ashirin ne kacal cikin dari na wadanda suka rubuta jarabawar suka sami sakamako mai kyawu a darusa biyar da suka harda Ingilishi da Lissafi, yadda zasu iya shiga jami'a, abinda wasu ke ganin akwai bukatar gyara.

Nijeriya dai dade tana fuskantar matsala a fagenta na ilmi abinda ke bada gudummawa wajen koma-bayan al'amurra a kasar.