Mahimman abubuwan da su ka faru a duniya 2010

Kusan dai za a iya cewa an fara shekarar 2010 ne da kafa wani sabon tarihi.

Wannan tarihi kuwa shi ne kaddamar da ginin Burj, ginin da ya fi kowanne gini tsawo a fadin duniya wanda aka gina shi a birnin Dubai na hadaddiyar daular larabawa. An dai fara ginin ne a dai dai lokacin da ake ganin bunkasar da aka samu a tattalin arzikin kasar, sai dai, an kaddamar da ginin ne a dai dai lokacin da aka fara fuskantar matsalar koma bayan tattalin arziki a kasashen duniya.

Tsuke bakin aljihu

A kasar Girka, a watan Mayun shekarar ta 2010, an yi ta tada jijiyar wuya ne biyo bayan daukar matakin tsuke bakin aljihu da gwamnatin kasar ta yi.

Manufar shirin dai ita ce zabtare yawan kudaden da gwamnati ke kashewa, wanda kuma a maimakon haka, aka baiwa kasar tallafin dala biliyan dari da hamsin.

Wata guda bayan haka kuma, ma'aikata ne a kasar Spain suka yi zanga zanga a manyan titunan kasar don nuna adawar su da rage kashi biyar cikin dari na albashin ma'aikata.

Abubuwan da su ka shafi addini

Har ila yau, a shekarar 2010 ne kasashen Faransa da Belgium suka kasance kasashen farko a nahiyar turai da suka haramta sanya nikabi a bainar jama'a.

Baya ga wadannan abubuwa da suka wakana, an kuma ga yadda cocin Roman Katolika ya fuskanci matsin lamba sakamakon zargin da aka yi wa wasu masu wa'azin addinin kirista na cocin da aikata fyade, lamarin da yasa har wani babban Bishop na cocin dan asalin kasar Belgium ya fito fili, inda ya amince cewa ya ci zarafin wani dan karamin yaro, kana daga bisani, Bishop din yayi murabus daga mukaminsa.

A karon farko da Paparoma Benedict ya kai ziyara tun bayan shekarar 1982 a Burtaniya a watan Satumba, an yi ta tambaya akan ko Paparoman zai fito fili ya nemi afuwa a madadin daukacin mabiya darikar Roman Katolika, kuma daga karshe, Paparoman ya fito fili inda ya nemi gafara akan haka.

Zabuka

A watan Mayun shekarar 2010 ne kuma hankula suka karkata zuwa Burtaniya bisa wasu dalilai.

Image caption David Cameron

Wadannan dalilai kuwa su ne manyan zabubbukan kasar da aka gudanar.

Bayan data shafe shekaru goma sha uku tana jan ragamar shugabancin kasar, jam'iyar Labour ta sha mummunar kaye a zaben. Koda yake babu jam'iyar da ta samu rinjaye.

Sai dai jam'iyar Conservative ita ce ta lashe akasarin kujeru, inda a karon farko cikin shekaru sittin da biyar- kasar ta Burtaniya ta samu gwamnatin hadin guiwa.

Prime Minista David Cameron, wanda mataimakinsa Nick Clegg, dan Jam'iyar Liberal Democrat ya rufa masa baya, ya yiwa manema labaru jawabi:

"Ina so mu sanya babancin jam'iyya a gefe domin mu ciyar da Burtaniya gaba, mun gama duk tattaunawar da ya kamata tsakanin jam'iyyun biyu domin mu samu gwamnatin hadin guiwa mai dorewa."

A dai-dai lokacin da al'ummomin kasar Holland suka kada kuri'a, jam'iyar dake adawa da addinin Musulunci, kusan ta nunka yawan kujerun da take da su a majalisun dokokin kasar, kana kuma an ga ci gaba a jam'iyar dake adawa da baki 'yan kasashen waje a zabukan da aka gudanar a kasar Sweden.

Haka zalika, bayan shafe shekaru goma sha takwas cur yana rike da madafun iko, an tilasta wa magajin garin Moscow, Yuri Luzhkov, sauka daga kan mukaminsa, inda kuma a cikin shekarar ta 2010 aka ga kyautatuwar dangantaka tsakanin Rasha da Poland.

Baya ga wannan, Kasashen Rasha da Poland sun shiga cikin wani hali na jimami sakamakon mutuwar shugaban kasar Poland Leh Kacinski, a wani hadarin jirgin sama da ya rutsa da shi tare da wasu manyan jami'an gwamnatinsa, a yammacin kasar Rasha.

A kasar Turkiya kuwa, Prime Ministan kasar Recip Tayyip Erdowan ne ya bayyana sakamakon zaben raba gardama akan kundin tsarin mulkin kasar da cewa wani gagarumin tarihi ne da aka kafa, inda muhimman sauye-sauye ta fuskar shari'a suka maida sojojin kasar yin biyayya ga kotunan fararen hula, a wani mataki na ganin an yi adalci ga jama'a.

A Burtaniya ma batun tabbatar da cewa anyi adalci ya yi kane-kane lokacin da tsohon Pirayim Ministan kasar Tony Blair, ya bada shaida a gaban hukumar bincike kan yakin kasar Iraqi.

Masu zanga zanga dai sun fito fili don bayyana matsayinsu a harabar zauren da Mr Blair ke bada shaida, inda ya amince cewa gwamnatinsa ta kasa hangen irin manyan matsalolin da suka dabaibaye kasar Iraqi bayan shekarar 2003.

Sai dai ya kafe cewa, shawarar da aka dauka ta abkawa Iraqi, shawara ce data dace: " Na yi amanar cewa da mun bar Sadam a kan mulki, dole ne zai zamar mana kayan baya a nan gaba, kuma za mu yi da -na-sani"

To ko me ya saura a Iraqi a shekarar ta 2010 ?

Zabubbukan 'yan Majalisu da ba a kai ga kammalawa ba a watan Maris sun haifar da shafe watanni takwas na rashin tabbas ta fuskar siyasa.

Sai dai a watan Nuwamba, dukkanin bangarorin sun amince su kulla yarjejeniyar raba madafin iko, inda aka zabi Nouri AL-Maliki a matsayin Prime Minister.

Sai dai daidaita tsakanin bangarorin ba karamin aiki bane.

Hare-haren kunar bakin wake sun ci gaba, inda a watan Oktoba aka halaka mutane 52 lokacin da wasu 'yan bindiga suka abka wa wani coci a birnin Bagadaza.

An dai bayyana wannan hari a matsayin wani mummunan bala'in da ya abkawa Kiristoci a kasar Iraqi a 'yan shekarun nan.

Haka zalika, a watan Agustan shekarar 2010 ne Amurka ta fara janye sojojinta a Iraqi kamar yadda aka shirya, inda wani sojan Amurka, lokacin da yake ketare kan iyakar Iraqi zuwa kasar Kuwait, ya numfasa tare da bayyana jin dadinsa.

Tattaunawa tsakanin Israila da Palasdinawa

A watan Satumban shekarar 2010 ne kuma aka gudanar da tattaunawa ta gaba da gaba tsakanin shugabannin Israila da Palasdinawa.

Image caption Sojojin Isra'ila a jirgin Flotilla

Sakatariyar harkokin wajen Amurka HIllary Clinton ta shiga cikin tattaunawar, inda Amurka ta yi ta matsin lamba na ganin an cimma yarjejeniya.

Kamar dai sauran lokuta, batun fadada matsugunan Yahudawa a yankunan Palasdinu ya zamo babban kalubale, sai dai an sake sabunta dakatar da gine-gine da Israila ke yi, inda Prime Ministan Israila Benjamin Netanyahu, ya bukaci Palasdinawa da kada su kaurace wa tattaunawar. To sai dai a watan Oktoban shekarar 2010, tattaunawar ta gaba da gaba ta sukurkuce, domin kuwa a farkon shekarar, batun ci gaba da gine gine ya sa dangantaka tsakanin Amurka da Israila tayi tsamin da ba'a taba ganin irinta ba, bayan da Israila ta sanarda gina wasu sabbin gidaje dubu daya da dari shida a yankunan Palasdinawa da ta mamaye.

Wannan al'amari dai ya sa sai da aka shafe wasu watanni ana ta kamun kafa ta fuskar Diplomasiya, kafin a iya sasanta tsakanin kasashen biyu wadanda suka dade suna kawance.

Dangantaka tsakanin Israila da Turkiya

Sai dai kuma a shekarar ta 2010 ne, dangataka tsakanin Israila da wata kasa da suka dade suna kawance wato kasar Turkiya ta sukurkuce.

"Kuna tunkarar yankin da ake fama da rigingimu a cikinsa, wanda kuma sojojin ruwa suka hana wucewa, an rufe gabar tekun dake Gaza ga duk masu zirga zirga ta jiragen ruwa."

Wannan sanarwa ce ta gargadi da sojojin Israila ke yi wa wani jirgin ruwan kasar Turkiya Flotilla, wanda ke dauke da kayayyakin agaji da kuma daruruwan 'yan rajin kare hakkin bil'adama wadanda ke goyon bayan Palasdinawa, da ke kan hanyar su ta zuwa Gaza.

A yayin da Sojojin Israila suka isa kusa da daya daga cikin jiragen ruwan, a wani dan karamin jirgi, matukin jirgin yayi ta gargadi ga wasu daga cikin fasinjojin dake cikin jirgin:

"Don Allah 'yan uwa, ku koma ciki ku zauna a kujerunku, ku daina gardama don suna amfani ne da harsashi na gaske, kuma ba zamu iya kare kan mu ba daga gare su."

An dai halaka mutane 9 'yan kasar Turkiya, sai dai an samu wasu rahotannin dake cin karo da juna game da gaskiyar abin da ya faru, inda dukkan bangarorin biyu suka yi ta zargin juna.

Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci da a gudanar da bincike na musamman, wanda kuma sai bayan wasu watanni ne jami'an Turkiya dana Israila suka yi wata ganawa don dinke barakar dake tsakaninsu.

A watan Nuwamba ne kuma aka gudanar da zaben Majalisun dokoki a kasar Masar.

A zagayen farko na zaben, jam'iyar dake mulki ta shugaba Hosni Mubarak ta lashe kusan dukkanin kujerun inda a bangare guda kuma- jam'iyar adawa da aka haramta a kasar ta rasa dukkanin kujerunta.

An dai yi ta sukar yadda aka tafka magudi a zaben.

'Yemen' kasar da kungiyar Al-Qaida ke tasiri

Haka kuma, kusan za a iya cewa an shafe shekarar 2010 ne inda ake ta nuna damuwa game da yadda ake amfani da kasar Yemen a matsayin sansanin kungiyar Al-Qaida, inda aka kame wasu kunshin sakwanni a cikin jiragen sama biyu na Amruka wadanda bincike ya nuna cewa an aike da sakwannin ne daga Yemen.

Hakan dai ya haifar da fargaba ta fuskar tsaro a kasashen Amurka da Burtaniya da kuma Gabas ta tsakiya.

A farkon shekarar 2010, Amurka ta sanar da cewa zata rubanya taimakon da take baiwa kasar Yemen don bunkasa kokarin da kasar ke yi na yaki da ta'addanci.

Amurka ta kuma kara baiwa Pakistan taimako, kasar dake da matukar muhimmmaci a yankin, a yakin da Amurkan ke yi da ta'addanci.

Ambaliyar ruwa a Pakistan

Haka zalika a watan Ogustan shekarar 2010, ambaliyar ruwa ta mamaye wasu yankuna da dama na kasar Pakistan.

Wannan dai ita ce ambaliyar ruwa mafi muni da aka taba gani a kasar cikin shekaru da dama, lamarin da ya sa fiye da mutane miliyan daya da rabi suka shiga cikin wani mayuwacin hali:

"Na ji yadda ruwa ke ta ambaliya, da na duba waje, sai naga ruwa ya mamaye kan titi ya nufi gidajen mu. Da muka ga haka, abin da muka iya yi shi ne kawai muka dare saman rufin gidajen mu."

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana ambaliyar ruwan da cewa ita ce bala'i mafi muni da aka taba gani a kasar.

Ga kasar Sri Lanka kuwa, shekarar 2010 ta fara ne da zaben shugaban kasar na farko tun bayan kawo karshen yakin basasar kasar.

Daga karshe dai, shugaban kasar dake kan karagar mulki a lokacin, Mahinda Rajapaksa shi ne ya lashe zaben, sai dai an tsare abokin takararsa General Sarath Fonseka, wanda kuma daga bisani aka tuhume shi da karya ka'idojin shigowa da makamai, tare kuma cusa kai a harkokin siyasa a lokacin da yake sanye da kayan sarki.

Ga kasar da ta ke kan gaba a nahiyar Asiya ta fuskar tattalin arziki kuwa wato kasar Sin, batun bada lambar yabon zaman lafiya ta Nobel da aka baiwa dan rajin kare hakkin bil'adama Liu Shabo, na daga cikin batutuwan da suka yi kane-kane a kasar.

Kasar ta Sin din dai ta yi gargadi ga dukkan kasashen dake halartar bukin, inda kuma ta yi zargin cewa an bada lambar yabon ne don cimma wata manufa ta siyasa.

Koriya ta kudu da ta Arewa

Hakazalika a cikin shekerar, an yi ta tada jijiyar wuya sakamakon harin da Koriya ta Arewa ta kai a wani tsibiri dake koriya ta kudu, kamar yadda mai magana da yawun gwamnatin Koriya ta kudu, Hong Sang-Pyo ya ce.

Kasar Koriya ta kudu ta dage cewa koriya ta arewa ce ta fara kai mata hari, lamarin da yayi sanadiyar mutuwar sojojin koriya ta kudun su biyu, yayin da kuma wasu da dama suka samu raunuka.

Wannan dai ita ce rigima kan iyokoki mafi muni da aka taba gani tun bayan yakin Korea da aka yi a shekarar 1953.

Zaben Burma

A kasar Burma kuwa, an gudanar da babban zaben kasar na farko ne cikin shekaru ashirin.

Babbar jam'iyar adawa ta National League for Democracy, jam'iyar da Aung San Suu Chi ke jagoranta ta bukaci masu kada kuri'u dasu kauracewa zaben.

An dai bayyana cewa jam'iyar dake samun goyon bayan gwamnatin sojan kasar ita ce ta samu gagarumin rinjaye. Sai dai bangarori da dama sun yi zargin cewa an tafka magudi.

Kwanakin kadan bayan zaben ne aka saki Aung San Suu Chi daga daurin talala da aka yi mata.

Rasuwar Shugaban Najeriya

Image caption Marigayi, Shugaba Umaru Musa Yar'adua

Ga kasar da ta fi kowacce kasa yawan jama'a a nahiyar Afrika kuwa, wato Najeriya, ta fara shekarar 2010 ne cikin wani yanayi na rashin tabbas dangane halin da shugaban kasar a lokacin ke ciki.

A lokacin dai, an yi amannar cewa marigayi Umaru Musa Yar'Adua na jinya ne a kasar Saudiyya inda daga bisani kuma- Allah yayi masa rasuwa a watan Mayu, wanda hakan ya baiwa mataimakinsa Goodluck Jonathan damar darewa kan karagar mulkin kasar.

A watan Okotoba na shekarar 2010 ne kuma Najeriyar ta cika shekaru 50 cif cif da samun 'yancin kai, sai dai kash!

Tashin wasu bama-bamai a Abuja babban birnin kasar ya rage tagomashin bukukuwan da aka shirya gudanarwa a ranar.

Akalla mutane 12 ne dai aka bayyana cewa sun rasu a tashin bama-baman.

Haka kuma a farkon shekarar, rikice-rikicen kabilanci da na addini sun mamaye batutuwan da ake tattaunawa akai.

An dai yi arangama a garin Jos tsakanin mabiya addinin Musulunci da mabiya addinin kirista, lamarin da yayi sanadiyar mutuwar daruruwan jama'a.

A kasar Rwanda kuwa, a shekarar 2010 ne aka gudanar zaben shugaban kasar wanda shugaban dake karagar mulki, Paul Kagame ya lashe.

Rikicin shugabanci a Ivory Coast

A kasar Ivory Coast kuwa, an gudanar da zaben shugaban kasar ne da fatan cewa zai kawo karshen rikice-rikicen da aka shafe shekaru 15 ana fama dasu a kasar, sai dai a maimakon hakan, zaben ya sake ruruta wutar rikicin da aka yi fama da shi ne a baya, inda 'yan takara biyu da suka fafata ke ikirarin samun nasara.

Majalisar Dinkin Duniya ta bi sahun sauran kasashen duniya wajen kira ga Laurant Gbagbo da ya sauka daga karagar mulkin kasar, don mutunta zabin jama'ar kasar.

Ita kuwa kasar Sudan, kasar da ta fi kowacce kasa girma a nahiyar Afrika ta gudanar da zaben shugaban kasa ne da jam'iyu da dama suka fafata wanda kuma shi ne irinsa na farko a kasar cikin shekaru da dama.

Kamar dai yadda aka yi ta hasashe, shugaban kasar mai ci Omar el Bashir ne ya lashe zaben.

Sai dai wani batu kuma ya mamaye fagen siyasar kasar.

Ana shirin gudanar da zaben raba gardamar a farkon shekarar 2011, kusan dai za a iya cewa kasar ta Sudan ta kammala shekarar ce inda take dab da samun wani gagarumin chanji.

Afrika ta kudu; Rarrabuwar kawuna a ANC

Ga kasar Afrika ta kudu kuwa, an fara shekarar 2010 ne da rarrabuwar kawuna tsakanin 'ya'yan jam'iyar ANC mai mulki.

Bangaren dake adawa da shugaba Jacob Zuma na zargin shugaban kasar da juyawa 'yan kungiyar kwadago baya.

Haka kuma, dangantakar dake tsakanin jam'iyar ANC da kungiyar kwadago ta sukurkuce lokacin da dubban ma'aikata suka shiga wani yajin aiki na sai abin da hali yayi kan batun karin albashi.

Ma'adinan lu'ulu'u su ne aka yi ta tafka muhawara akai a shari'ar da Naomi Campbell, wacce ke amfani da surar jikinta wajen tallace-tallace ta bada shaida a gaban kotun hukunta masu aikata laifukan yaki dake Hague a shari'ar da ake yi wa tsohon shugaban kasar Laberia Charles Tailor.

An yi zargin cewa Miss Campbell ta karbi wasu ma'adinan lu'ulu'u a matsayin kyauta ne daga hannun Mr Taylor a kasar Afrika ta kudu a shekarar 1997, zargin da ta musanta.

Girgizar kasa a Haiti

A cikin wani yanayi na jimami ne al'ummomin kasar Haiti suka fara shekarar 2010, inda fiye da mutane dubu 30 suka mutu lokacin da kasar ta yi fama da bala'in girgizar kasa mafi muni da ta abkawa kasar cikin shekaru 200.

"Mutane da dama sun mutu, muna matukar bukatar taimako daga kasashen duniya, babu wani taimako, ba asibiti, ba wuta, ba abinci ba ruwa kusan dai ba komai."

Lokacin da annobar cutar kwalara ta bulla a watan Oktoba, fargabar ita ce, ko cutar zata yadu a wuraren da aka tanadar wa dubban 'yan kasar da suka rasa muhallansu sakamakon girgizar kasar.

Annobar ta yi sanadiyar mutawar fiye da mutane dubu daya lamarin da ya haifar da zanga-zanga.

Safarar miyagun kwayoyi a Mexico

Ga kasar Mexico kuwa, wani abu da ya mamaye shekarar 2010 shi ne tashe-tashen hankula daga kungiyoyin dake safarar miyagun kwayoyi.

An kuma gano wani makeken rami da ake binne gawarwakin mutane, da kuma karuwar kisan gilla da ake yi wa jama'a.

Da yake kare matakan da gwamnatinsa ke dauka, shugaban kasar Felipe Calderon, ya amince cewa an samu karuwar tashe tashen hankula: "Wannan kusan za a iya cewa saboda ana samun karuwar kazamin fada tsakanin kungiyoyin dake adawa da juna akan mallakar kasuwanni ko kuma wasu hanyoyi."

Hadin kai maimakon rarrabuwar kawuna na daga abubuwan da aka gani a kasar Chile lokacin da miliyoyin 'yan kasar a sassa daban-daban na duniya suka shiga wani yanayi na kaduwa, sakamakon halin da mahaka ma'adinai su 33 suka shiga.

Su dai mahaka ma'adinan da suka shafe fiye da watanni 2 a cikin kogon da ya rufta dasu, daga karshe Allah yayi musu gyadar dogo, inda aka fiddo su daya bayan daya da ransu.

A kasar Ecuador kuwa, an ga wani yanayi ne da aka kwatanta shi da cewa tamkar wasan kwaikwayo ne da ya faru a kasar bayan da sojoji suka kubutar da shugaban kasar Rafael Correa daga wani asibiti.

Shi dai Rafael Correa ya nemi mafaka ne bayan da wasu bijirarrun 'yan sanda suka harba masa hayaki mai sa hawaye, inda daga bisani aka sanya dokar ta baci.

Ita kuwa kasar Brazil, a shekarar 2010 ne ta yi adabo da shugaban kasar daya fi kowane shugaba da aka taba yi a kasar farin jini Luiz Inacio Lula da Silva.

Shi dai Mr da Silva ya daga martabar kasar a idon duniya lokacin da yake jan ragamar shugabancin kasar.

Ita kuwa kasar Cuba, shekarar 2010 shekara ce da aka ga sauyi a tsarin yadda ake tafiyar da tattalin arzikin kasar, inda gwamnati ta shirya korar wasu ma'aikata da dama a wani mataki na kokarin farfado da tattalin arzikinta.

Sauye-sauye a Amurka

Ita kuwa Amruka ta ga wasu muhimman sauye sauye ne tsarin yadda ake tafiyar da harkokin bankunan dake kasar.

Baya ga wannan, an kuma ga wani gagarumin sauyi a tsarin kula da lafiyar jama'a a kasar, bayan garanbawul din da shugaba Obama yayi a bangaren kiwon lafiya.

Bayan da aka shafe shekara guda ana tafka zazzafar muhawara, tare da fuskantar adawa mai karfi daga bangaren 'yan jam'iyar Republican, a karshe, an amince da dokar da nufin baiwa karin Amurkawa miliyan 30 ingantaccen tsarin inshora ta fuskar kiwon lafiya.

Baya ga wadannan abubuwa, shugaba Obama ya fitar da sabon tsari ta fuskar tsaron kasar wanda ya takaita yanayin da zai sa Amurka tayi amfani da makaman nukiliya.

Malalar mai a tekun Mexico.

A ranar 20 ga watan Aprilu ne kuma daya daga cikin rijiyoyin mai na kamfanin BP ya fashe, inda ma'aikata 11 suka rasa ransu.

Daga ranar da alamarin ya faru zuwa watan Yuli, an kiyasta cewa kimanin galan-galan na danyen mai miliyan 20 ne ya yi ta malala a tekun Mexico, lamarin da ya kai ga shafar masu sana'ar kamun kifi a tekun.

Kamfanin mai na BP ya fuskanci fushin Amurkawa, inda ita ma gwamnati Amurkan, aka yi ta sukar ta kan irin matakan da ta dauka.

Shugaba Obama ya kuma fuskanci wani koma baya a cikin shekarar lokacin da 'yan jam'iyar Republican suka sami gagarumin rinjaye a zaben rabin wa'adin mulki, lamarin da ya basu damar karbe ragamar shugabanci a majalisar wakilan kasar.

Wikkileaks: kwarmata bayanai

Wasu 'yan makwanni bayan afkuwar wannan al'amari dai, an ajiye batun siyasar Amurka a gefe guda, inda batun tonon sililin da shafin yanar gizo na Wikkileak ya fitar na wasu takardun sirri daga jami'an diplomasiyyar Amurkan, ya zamo shi ne batun da ya yi kane-kane a kasar dama sassa daban-daban na duniya.

Shafin na Wikkileaks dai ya fitar da dubban takardun sirri ne, wadanda suka nuna wasu bayanai marasa dadi da aka yi game da shugabanni a kasashen duniya da kuma batutuwan da suka shafi danganta tsakanin kasashe daban-daban na duniya.

Ga abin da Mutumin da ya kirkiro shafin na Wikkileaks Julian Assange ke cewa:

"Gwamnati ce ke kokarin ganin hana mu damar wallafa takardun da suka dace, suna zasu hana mu damar wallafa kowadanne irin takardu."

Daga bisani dai kasar Sweden ta bada sammacin kame Mr Assange bisa zarginsa da aikata fyade, zargin da ya musanta.

Kana kuma a watan Decembar ne, aka cimma yarjejeniya a taron sauyin yanayi da Majalisar Dinkin Duniya ta shirya a wurin shakatawa na Cancun dake birnin Mexico.

Za mu kammala ne da Burtaniya inda shekarar 2010 ta kare da shirye-shiryen wani kasaitaccen bukin aure da za a gudanar a watan Aprilu shekarar 2011, wannan buki kuwa shi ne na mai jiran gadon sarautar Burtaniya Yarima Williams da dadaddiyar budurwarsa Katherine Middleton.