Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Sa-in-sa tsakanin 'yan siyasa a Ghana

A kasar Ghana wani abinda ake damuwa dashi yanzu a fagen siyasan kasar shine zage zage da bace bace da 'yan siyasan da magoya bayansu suke yima juna a duk wani abinda ya taso idan dai ya danganci siyasa.

Haka kuma ko wani lamari ne daban zai taso sai 'yan siyasan musamman daga bangarorin manyan jam'iyun siyasan kasar guda biyu wato da NDC mai mulki da NPP da 'yan adawa sai anyi mishi fasaran siyasa inda zaka ji suna maganganun batanci game da juna.

Lamarin ya kai har sai da shugaban kasar wato John Atta Mills ya gayyaci shugabannin addinin kasar don su taimaka mishi wajen ganin an shawo kan matsalar dake barazanan rarraba kawunan al'umman kasar.

Sai ku saurari rahoton da Iddi Ali ya hada mana game da lamarin.