Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Muhimman abubuwan da su ka faru a Nijar 2010

Image caption A watan Fabrerun 2010 ne Salou Djibou ya zamo shugaban kasa bayan juyin mulkin da sojoji suka yi

A jamhuriyar Nijar, shekarar da ta gabata ta kafa tarihi mai yawa kama daga juyin mulki da wasu sojoji suka yima gwamnatin Malam Mamadou Tandja, da matsalar yunwa da mutuwar dabbobi.

Ga ambaliyar ruwa da cabke wasu sojoji da hukumomin sojan Mulkin Sojan CSRD suka yi wadanda ake zargi da yunkurin hambarar da gwamnati.

Hakanan kuma wani muhimmin batu da ya ja hankalin 'yan kasar ta Nijar, shi ne na shirya zaben raba gardama a kan wani sabon kundin tsarin mulki mai ruwa biyu.

Wanda zai kawo karshen gwamnatin mulkin soja ta hanyar shirya zaben shugaban kasa a karshen wannan watan Janairun 2011.

Wakilin mu a Yamai Idy Baraou ya yi mana waiwaye adon tafiya, game da muhimman abubuwan da suka faru a kasar ta Nijar a cikin shekarar da ta gabata, ga kuma rahoto na musamman da ya aiko mana: