Sai a watan Maris za a yi wasan Chelsea da Man U

Chelsea da Manchester United
Image caption A ranar 19 ga watan Disamba aka so gudanar da wannan wasa

Hukumar shirya gasar Premier ta Ingila, ta ce wasan da za a fafata tsakanin Chelsea da Manchester United, wanda kankara ta hana, za a yi shi ne a ranar 1 ga watan Maris na 2011.

Asali an shirya yin wasan ne a filin Stamford Bridge ranar 19 ga watan Disamba, amma sai aka dakatar saboda kankarar da ke zuba.

Sai dai, za a iya sauya ranar idan har daya daga cikinsu ya samu kansa a maimaicin zagaye na biyar na gasar FA.

Amma idan duka aka cire su kafin ranar, to za a maida wasan karshen makon da za a gudanar da wasan FA.