Za a ci tarar masu kula da filayen jirgi

Gwamnatin Birtaniya na tunanin bullo da wasu dokoki da zasu sa a rika cin tarar kampanonin kula da filayen jiragen saman da aka samu cikas a ayyukansu, sakamako rashin wani kyakkyawan tanaji a sakamon sauyin yanayi.

Sakatariyar kula da harkar zirga zirgar jiragen sama, Theresa Villiers ta ce akwai bukatar filayen jiragen saman su rika aiki yadda ya kamata, su kuma kasance cikin shirin ko-ta-kwana.

Wakilin BBC ya ce furucin Theresa Villiers ya zo ne mako guda bayan da aka rufe filin saukar jiragen sama na Heathrow, wanda ya fi kowane hadahadar pasinjoji a duniya,a sakamakon zubar dussar kankara.

An soke tashi da saukar jirage da dama, inda ta kai pasinjoji suka rika kwana a kasa a tasahar jiragen saman.

An zargi kampanin BAA mai kula da filin jirgin da gaza kashe kudi sosai wajen sayen na'urorin narkawa da kwashe kankara.