Za a ci tarar masu kula da filayen jirage a Burtaniya

Fasinjoji a filin jiragen sama na Heathrow
Image caption Fasinjoji sun kwana a kasa a filin jiragen sama na Heathrow

Gwamnatin Burtaniya na tunanin bullo da wadansu dokoki da za su sa a rika cin tarar kamfanonin kula da filayen jiragen saman da aka samu cikas a ayyukansu, sakamakon rashin kyakkyawan tanadi don tunkarar sauyin yanayi.

Sakatariyar kula da harkar zirga zirgar jiragen sama, Theresa Villiers, ta ce akwai bukatar filayen jiragen saman su rika aiki yadda ya kamata, su kuma kasance cikin shirin ko-ta-kwana.

Furucin na Theresa Villiers ya zo ne mako guda bayan da aka rufe filin saukar jiragen sama na Heathrow, wanda ya fi kowanne hadahadar fasinjoji a duniya, sakamakon zubar dusar kankara.

An soke tashi da saukar jirage da dama, al'amarin da ya kai fasinjoji na kwana a kasa.

An zargi kamfanin BAA mai kula da filin jirgin da gazawa wajen kashe kudi sosai don sayen na'urorin narkawa da kwashe kankara.