Faransa ta kama jirgin saman Laurent Gbagbo

Laurent Gbagbo
Image caption Laurent Gbagbo

Hukumomin Faransa sun rike wani jirgin sama na shugaban Ivory Coast wanda ya ki sauka daga mulki, Laurent Gbagbo.

Ma'aikatar wajen Switzerland ta ce jirgin saman ya shafe kwanaki da dama a tsaye a filin jirgin saman Basel-Mulhouse, wanda ke karkashin kulawar hukumomin Faransar da na Switzerland.

Mista Gbagbo dai ya ki amincewa da sakamakon zaben shugaban kasa zagaye na biyu wanda a kasashe da dama aka yi imanin cewa abokin adawarsa Alassane Ouattara ne ya lashe shi.

Wata tawagar shugabannin Afirka na shirin zuwa kasar ta Ivory Coast ranar Talata domin shawo kan Mista Gbagbo ya sauka.

Sai dai wani kakakinsa, Yao Gnamien, ya ce, "ina tsammanin wannan tawaga ba za ta zo ne ta nemi Shugaba Gbagbo ya sauka ba.

"Za ta zo ne, a tsammanina, domin ta fahimci abubuwan dake gudana".

Karin bayani