Rikicin Jos ya kara rincabewa

'Yan sanda a garin Jos
Image caption 'Yan sanda a garin Jos, babban Jihar Filato, Najeriya

Rahotanni daga Jos, babban birnin jihar Filato, sun nuna cewa al'amura sun kara rincabewa yau Lahadi, inda aka sami asarar rayuka da dukiya sakamakon wani sabon tashin hankali.

Sabon tashin hankalin dai ya fi kamari ne a unguwannin Dutse Uku, da Unguwar Damisa, da Dogon Karfe da Rikkos da Unguwar Rukuba da mahadar hanyar Tina wadanda wurare ne da Musulmi da Kirista ke makota a tsarin zaman birnin na Jos.

Kwamandan runduna ta musammam mai aikin samar da tsaro a jihar Filato, Birgediya Janar Hassan Umaru, ya tabbatarwa da wakilin BBC aukuwar lamarin; a cewarsa, an girke karin dakaru a unguwannanin da lamarin ya yi kamari domin shawo kan al'amarin.

Da aka tambaye shi ko mutane nawa ne suka rasa rayukansu, sai ya ce ba zai ce kome kan wannan ba a yanzu.

Shi kuwa kwamishinan 'yansandan Jihar, Abdulrahman Akano, da aka tuntube shi ta waya, sai mataimakinsa na musamman ya bayyana cewa suna wani taro a kan lamarin da gwamnan jihar ta Filato, Jonah Jang.

To sai dai kuma wasu mazauna birnin na Jos sun bayyana cewa sun ga gawarwakin mutane da kuma wadanda aka jikkata.

Sabon tashin hankalin na yau dai ya barke ne sakamakon rashin jin dadi da wasu matasa suka nuna wadanda suka ce harin bama-baman da aka kai a jajibirn Kirismeti ya yi sanadiyar mutuwar 'yan uwansu, don haka suka dauki mataki na ramuwa a kan al'umar da suke zargi da tayar da bama-baman; ko da yake dai gwamantin jihar da kuma hukumomin 'yansanda sun ce tashin bama-baman wani lamari ne na siyasa ba na addini ba.