Jam'iyyun Ivory Coast sun yi kiran yajin aiki

Alassane Ouattara
Image caption Mutumin da duniya ta yi imani ya lashe zaben Ivory Coast, Alassane Ouattara

A kasar Ivory Coast, jam'iyyun siyasar da ke goyon bayan mutumin da kasashen duniya suka yi amannar cewa shi ne ya lashe zaben shugaban kasar, Alassane Ouattara, sun yi kiran da a fara yajin aiki daga yau Litinin har sai Laurent Gbagbo ya sauka daga karagar mulki.

A wata sanarwa da ta fitar, jam'iyyar Mista Ouattara ta nemi jama'a da kada su bari a kwace nasarar da suka samu.

Tun da farko, kungiyar ECOWAS ta gargadi Mista Gbagbo ya sauka tun da girma da arziki ko kuma a yi amfani da karfin soji a hambarar da shi.

Sai dai a nasa bangaren, Mista Gbagbo ya ce makirci ne kawai na kasashen Faransa da Amurka wadanda ke son a sauke shi daga karagar mulki.

Kiran gudanar da zanga-zanga ya jaddada kiraye-kirayen da wanda ake tsammanin zai zama Firayim Ministan Mista Ouattara ya yi a makon jiya, kuma yin hakan zai durkusar da tattalin arzikin kasar, wanda tun farko rikicin ya ke tangal tangal.

Karin bayani