Musulmai za su iya kasuwanci a kasuwar hannyen jari ta Mumbai

Wasu jami'ai na kasuwar hannun jari ta Mumbai
Image caption Wasu jami'ai na kasuwar hannun jari ta Mumbai

Kasuwar hada-hadar hannayen jari ta Bombay da ke birnin Mumbai na India ta kaddamar da wani sabon rukunin kamfanoni da ayyukansu suka dace da sharuddan addinin Musulunci.

Kasuwar ta bullo da TASIS Shariah 50 ne a hanyar amfani da shawarwarin da ta samu daga wata Hukumar shariar musulunci ta India.

Wani bincike dai ya gaano cewa galibin Musulmai a India ba sa harka da tsarin hada-hadar kudade na Hukuma saboda tsarin shariar Musulunci ya harmata wa musulmai su zuba jari a kamfanonin da sayer da kayyaki irinsu barasa da taba sigari da makamai ko kuma kamfanonin da ke aiki da riba.