Muna bukatar yin azama - in ji Ancelotti

Carlo Ancelotte
Image caption Manajan Celsea Ancelotti ta shiga damuwa

Manajan kulab din Chelsea, Carlo Ancelotti ya shaida wa `yan kulab din cewa akwai bukatar su farka kafin su cire-rai da kare kambinsu na firimiya.

Kulab din ya sha kaye a hannun kungiyar Arsenal ranar litinin din da ta wuce, inda Arsenal ta ci shi uku da daya, kuma sau shida kenan yana shan kaye a wasannin lig, lamarin da ya maida shi na hudu a teburin gasar.

Rabon kulab din Chelsea da samun nasara tun wanda kulan din ya samu a ranar goma ga watan Nuwamban da ya wuce a wasan da ya yi da kungiyar Fulham.

Ancelotti dai yana nuna damuwa ne dangane da matsayin kulab din nasa, yana cewa "na damu matuka, saboda wasanni shida kenan muka yi ba tare da wata nasara ba."